Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Moscow Ta Tuna Da Rikicin Garkuwa Da Mutane A Gidan Wasa A 2002 - 2003-10-24


Hukumomin Rasha sun gudanar da bukin cikar shekara guda da mummunan rikicin yin garkuwa da mutane a wani gidan wasa da sinima na birnin moscow, inda a jiya alhamis suka bude wani dogonyaro na tunawa da wadanda suka mutu a wurin.

Shugaba Vladimir Putin ya ajiye furanni, yana mai fadin cewa wannan harin yin garkuwa da mutanen ya tayar da wani mikin da za a jima bai warke ba.

A ranar 23 ga watan Oktobar 2002, 'yan tawayen Chechnya su 41 dauke da makamai sun abka cikin gidan wasannin inda mutane kusan 800 suke kallon wani wasan kwaikwayo na waka. Sun yi garkuwa da mutanen na tsawon kwanaki biyu suna neman da Rasha ta janye baki daya daga Chechnya.

'Yan sanda sun dura wata iskar gas mai sanya barci cikin wannan gidan wasa domin luguiguita 'yan tawayen na Chechnya kafin sojoji su abka ciki. Iskar gas din ta kashe 'yan tawayen, amma kuma ta kashe fararen hula 130 daga cikin mutanen da ake yin garkuwa da su.

XS
SM
MD
LG