Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Aikin Agaji Suna Ci Gaba Da Fatan Ceto Masu Hakar Ma'adinai Na Rasha A Karkashin Kasa - 2003-10-28


Masu aikin agaji a yankin kudancin kasar Rasha, suna ci gaba da kokari ba dare ba rana domin ceto ma'aikatan hakar ma'adinai su 13 daga wani ramin hakar kwal, kafin ruwa ya cike wannan rami baki daya.

Tun ranar alhamis wadannan ma'aikatan hakar ma'adinai suke toshe mita 800 a karkashin kasa a garin Rostov-on-Don.

Kungiyoyi biyu na masu aikin ceto suna gudanar da wannan aiki. Kungiyar farko tana tona rami zuwa inda mutanen ke toshe daga wani ramin tonon ma'adinai dake daura da wannan. Kungiya ta biyu kuma tana kokarin zuba daruruwan ton na duwatsu a cikin ramin hakar kwal din domin hana ruwan dake fitowa daga wata korama ta karkashin kasa shiga tare da rufe inda ma'aikatan suke makale a cikin ramin.

Hukumomi ba su samu tuntubar ma'aikatan ba, amma kuma sun ce har yanu suna fatar za a iya ceto su da rayukansu.

XS
SM
MD
LG