Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Bayar Da Agaji Ga Jihar California... - 2003-10-28


Jami'ai a Jihar California dake nan Amurka sun ce wutar daji a yankin kudancin jihar ta kashe mutane akalla 14, ta kuma lalata gidaje fiye da dubu daya.

Suka ce wutar dajin, wadda ta kama a wurare da dama a makon jiya, tana yin barazana har yanzu ga dubban gidaje a kewayen birnin Los Angeles.

'Yan aikin kwana-kwana suna yakar wannan wuta a yayin da ake fama da iska mai karfi dake dada hura wutar, ga kuma zafi da rashin ruwan sama.

Shugaba Bush ya ayyana wasu kananan hukumomi hudu a kudancin jihar California a zaman yankunan dake fama da bala'i, matakin da zai ba su damar samun agajin gwamnatin tarayya.

Jami'ai suna neman wasu mutane biyu wadanda ake zaton sun tayar da daya daga cikin wutar dajin da gangan a yankin karamar hukumar San Bernardino.

XS
SM
MD
LG