Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Ta Damu Da Dakatar Da Aikin Rigakafin Cutar Shan Inna A Arewacin Nijeriya - 2003-10-28


Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kawo cikas ga kyamfe dinta na allurar rigakafin cutar shan inna a Nijeriya, yana yin barazana ga yankin Afirka ta Yamma baki daya.

Hukumar ta MDD ta fada a jiya litinin cewar wannan kokari na yin rigakafin yana fuskantar cikas a saboda kiyawar jama'a a yankin arewacin Nijeriya, inda akasarin jama'ar Musulmi suke, su rungumi wannan shiri na yaki da cutar shan inna.

Jihohi uku a arewacin Nijeriya, Kano da Kaduna da kuma Zamfara, sun jinkirta ko kuma dai sun ki bayar da iznin gudanar da wannan aiki, a bayan da wani sanannen malamin Addinin Musulunci ya ce watakila wannan ruwan maganin rigakafi yana tattare da hatsari.

Shugaban majalisar koli ta Shari'ar Musulunci a Nijeriya, Datti Ahmed, ya ce watakila an gauraya ruwan maganin rigakafin shan inna da kwayar halittar cutar nan ta HIV mai haddasa kanjamau, ko kuma da magungunan hana haihuwa. Ya ce ya kamata a dakatar da wannan aiki har sai jami'ai sun samu damar binciken wannan maganin.

Wani kakakin hukumar kiwon lafiya ta duniya ya ce Nijeriya ta fi kowace kasa yawan mutane masu fama da cutar shan inna a duniya. Ya ce ruwan maganin rigakafin ba ya tattare da wani hatsari.

A cikin 'yan kwanakin nan aka bayar da rahoton sabbin kamuwa da cutar shan inna a wasu kasashe hudu masu iyaka da Nijeriya, Ghana da Togo da Nijar da Burkina Fasso.

Ana rade-radi a Nijeriya cewar wannan aikin rigakafi wata makarkashiya ce da kasashen yammaci suka kulla domin kayyade yawan jama'ar kasar ta hanyar yada cutar kanjamau ko kuma hana jama'a haihuwa.

XS
SM
MD
LG