Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yasser Arafat Ya Bukaci Qoreia Da Ya Ci Gaba Da Rike Mukamin Firayim Minista - 2003-10-29


Shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, ya bukaci Ahmed Qureia da ya ci gaba da rike mukamin firayim minista a bayn cikar wa'adinsa na wata guda a zaman shugaban majalisar zartaswa ta wucin gadi ta gaggawa a mako mai zuwa.

Ministan harkokin wajen Falasdinawa, Nabil Shaath, ya fadawa 'yan jarida a birnin Ramallah, cewar Malam Qureia ya yarda zai nada sabuwar majalisar zartaswa cikakkiya duk da sabanin ra'ayin da aka ce akwai a tsakaninsa da Malam Arafat kan wanda zai rike ikon bayar da umurni ga dakarun tsaron Falasdinu.

A nan Washington, shugaba Bush ya shaidawa 'yan jarida cewa abin takaici ne cewar tsohon firayim minista Mahmoud Abbas, ba ya rike da wannan mukami a yanzu. Mr. Bush ya ce bai ga alamar akwai kudurin yaki da ta'addanci daga wadanda ya kira tsoffin hannun Falasdinawa ba.

XS
SM
MD
LG