Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Daji Ta Tilasta Kwashe Dubban Mutane Daga Gidajensu A Jihar California - 2003-10-29


Jami'ai a Jihar California ta nan Amurka sun umurci mutane akalla dubu 20 da su fice daga gidajensu, a bayan da wutar daji ta kashe mutane akalla 16 a can.

Suka ce wannan wuta da ta fara ci a makon da ya shige, yanzu ta bazu zuwa cikin kasar Mexico, inda ta kashe mutane biyu a can.

Wannan wutar daji dake ci a wurare da dama daga yankin birnin Los Angeles a arewa zuwa cikin kasar Mexico a kudu, ta kona akalla kadada dubu 200 na filaye tare da gidaje akalla dubu daya da 500.

Masu aikin kwana-kwana sun bayar da rahoton samun wata 'yar nasara a jiya talata, a lokacin da suka shawo kan wutar dake barazana ga Simi Valley a kusa da birnin Los Angeles.

Jami'ai suka ce suna neman wasu mutane biyun da ake kyautata zaton sune suka tayar da daya daga cikin wutar da gangan. Ana sa ran gwamnan California mai jiran gado, Arnold Schwarzeneger, zai tattauna batun agajin gwamnatin tarayya a lokacin ziyarar da zai kawo nan birnin Washington a yau laraba.

XS
SM
MD
LG