Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Ta Bayar Da Umurnin A Binciki Maganin Rigakafin Cutar Shan Inna - 2003-10-31


Wani babban malamin addinin Musulunci a Nijeriya, yayi marhabin da shawarar da gwamnatin kasar ta yanke ta binciken maganin yin rigakafin cutar shan inna wanda ya ce yana tattare da hatsari.

Shugaban majalisar Koli ta Shari'ar Musulunci a Nijeriya, Datti Ahmed, ya ce kungiyarsa tana farin cikin ganin cewa gwamnati ta dauki mataki kan zargin da yayi cewar watakila an gurbata maganin rigakafin da cutar kanjamau ta AIDS, ko kuma dai an zuba wasu magunguna na hana haihuwa a ciki.

Kungiyarsu ta yi zargin cewa Amurka ta gurbata maganin a wani bangare na makarkashiyar kayyade yawan jama'ar Nijeriya.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, wadda take gudanar da shirin rigakafin, ta yi watsi da wannan zargi. Ta ce an gwada maganin kuma babu wani hatsarin da yake tattare da shi. Ana ci gaba da aikin rigakafin a wasu jihohin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Majalisar Dinkin Duniya ya ambaci Malam datti Ahmed yana fadin cewa, "muna farin ciki da gwamnati ta gano bukatar dake akwai ta binciken maganin rigakafin cutar shan innar." Amma kuma yayi kashedin cewa bai kamata a dora alhakin binciken magungunan a hannun kungiyoyin lafiya na kasa da kasa da suke gudanar da wannan aiki ba.

Mataimakin shugaban Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayar da umurnin da a gudanar da binciken wannan maganin rigakafi a bayan da wasu jihohi uku wadanda akasarin al'ummarsu Musulmi ne a arewacin kasar suka ki yarda a gudanar da wannan aikin a jihohinsu. Jihohin sune Kano da Kaduna da kuma Zamfara.

XS
SM
MD
LG