Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Ta Yamma Suna Kokarin Farfado Da Shirin Zaman Lafiya A Ivory Coast - 2003-10-31


Shugabannin Nijeriya da Ghana sun tattauna da shugaban Ivory Coast a wani yunkuri na farfado da shirin zaman lafiya na kasar dake neman wargajewa.

Shugaba Olusegun Obasanjo da shugaba John Kuffour na Ghana sun tattauna da shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast jiya alhamis a birnin Abidjan.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaci shugaba Kuffour na Ghana yana fadin cewa shugabannin sun yi tattaunawa mai amfani. Shi ne shugaban kungiyar Kasuwar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma ta ECOWAS wadda ke jagoranci a kokarin warware rikice-rikicen yankin.

Mr. Kuffour ya ce watakila a wata mai zuwa za a sake gudanar da wani taron tattaunawa a tsakanin shugaba Gbagbo da 'yan tawayen Ivory Coast a kasar Ghana.

An sa ran cewa shugaba Obasanjo da shugaba Kuffour zasu matsawa shugaban Ivory Coast lamba kan ya gaggauta gabatar da sabuwar doka kan ka'idojin zamowa dan kasa da kuma mallakar filaye, kamar yadda aka yi tanadi cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da Faransa ta tsara tsakanin sassan, aka kuma rattabawa hannu a watan Janairu.

Har ila yau, yarjejeniyar ta bukaci Mr. Gbagbo ya raba ikon mulki tare da 'yan tawayen da sauran jam'iyyun adawa a gwamnatin rikon kwarya da za a kafa ta tsawon shekaru biyu.

Amma kuma, 'yan tawaye sun dakatar da shiga cikin harkokin gwamnatin a watan da ya shige, suna masu zargin Mr. Gbagbo da kin aiwatar da yarjejeniyar.

XS
SM
MD
LG