Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru Sun Ja Kunne Game Da Tsanantar Karancin Ruwa A Fadin Duniya - 2003-11-03


Wasu masana masu bincike na kasa da kasa sun yi kashedin cewa yawan ruwan sha mai kyau da ake samu zai ci gaba da raguwa a fadin duniya idan har gwamnatoci da kungiyoyi ba su takali wannan matsala ba.

Wakilan Kungiyar Bayar da Shawara kan Binciken Ayyukan Noma a Kasa da Kasa suka ce matsalar rashin wadatacciyar hanyar kula da ruwan sha ta fi muni a kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara.

Suka ce idan har ba dauki matakan kyautata hanyoyin samar da ruwan sha da kula da su ba, to wannan matsala zata kara muni a yayin da ake zaton nan da shekaru ashirin yawan ruwan da ake bukata zai ninku.

Haka kuma, sun yi gargadin cewa amfanin gonar da ake samu a nahiyar Afirka yana iya raguwa da kashi 25 daga cikin 100, watau rubu'i guda, a saboda karancin ruwan.

Ana sa ran cewa wakilan dake halartar taron kwanaki biyar da ake yi a Nairobin Kenya za su kaddamar da wani sabon shirin da zai nazarci matsalar karancin ruwa a fadin duniya. Gwamnatoci da cibiyoyi 64, cikinsu har da Bankin Duniya, suka samar da kudi dala miliyan 60 na gudanar da wannan shirin.

XS
SM
MD
LG