An kabo wani makeken jirgin saman helkwafta na sufuri na sojojin Amurka a Iraqi, inda aka kashe sojojin Amurka su akalla 15, wasu fiye da 20 kuma suka ji rauni.
Shaidu sun ce wadannan jiragen helkwafta kirar Chinook suna tafiya a jere a kusa da garin Fallujah, a lokacin da wasu makamai masu linzami akalla guda biyu suka harbi daya daga cikinsu. Wani kakakin rundunar sojojin Amurka ya ce ana binciken wannan lamarin.
A nan Washington, sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, ya bayyana kabo wannan jirgi a zaman mummunar rana ta alhini da bakin ciki ga Amurka, yana mai lasar takobin cewa za a murkushe wadanda suka harbo jirgin.
Wannan harin shi ne mafi muni da aka kai a kan sojojin Amurka tun lokacin da shugaba Bush ya ayyana karshen mummunan fada a Iraqi watanni shida da suka shige.
Hukumomin Amurka sun ce an kai hari kan wadannan jiragen helkwafta biyu dake dauke da sojoji daga runduna ta 82 ta mayakan sama a kan hanyarsu ta zuwa filin jirgin saman Bagadaza, daga inda za su tafi hutu.
A can wani gefen kuma, na kashe wani sojan Amurka jiya lahadi a Bagadaza, a lokacin da wani bam ya tashi a gefen hanya daidai lokacin da kwambar motocin sojoji ke shigewa.
A can garin Fallujah kuma, an kashe wasu Amurkawa fararen hula su biyu dake aiki ma rundunar injiniyoyin sojan Amurka a lokacin da bam ya tashi a gefen motarsu. Gidajen telebijin sun nuna 'yan Iraqi, cikinsu har da wani yaro dauke da hular kwano ta wani sojan Amurka, suna rawa da tsalle sun kewaye garwar motar.