Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Isra'ila Yana Adawa Da Kudurin MDD Kan Shirin Samar Da Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya - 2003-11-03


Firayim ministan bani Isra'ila, Ariel Sharon, an ce yana shirin kira ga shugaba Vladimir Putin na Rasha a yau litinin da ya janye wani kudurin da Rasha ta gabatar tana neman Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta yi na'am da "Taswirar Shimfida Zaman Lafiya a Gabas ta Tsakiya."

A makon da ya shige jami'an Rasha suka gabatar da daftarin kudurin gaban Kwamitin Sulhu suna neman wannan Kwamiti mai wakilai 15 ya fito ya bayyana goyon baya ga shirin a hukumce.

WAnnan shirin wanda Amurka da MDD da Tarayyar Turai da kuma Rasha suka zana, ya tanadi kafa kasar Falasdinu nan da shekara ta 2005.

Isra'ila ta ce a bisa manufa, tana goyon bayan shirin, amma kuma ta bukaci majalisar mulkin kan Falasdinawa da ta murkushe kungiyoyin dake kai hare-hare kan Isra'ila kafin a bayar da damar kafa kasar Falasdinu.

A halin da ake ciki, kungiyar Hamas ta bayyana a yau litinin cewar ba zata daina kai hare-hare kan fararen hular Isra'ila ba. Amma kuma ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa a shirye kungiyar ta masu kishin Falasdinu take ta takaita hare-hare kan fararen hular Isra'ila idan har Isra'ila ta daina jikkata fararen hula Falasdinawa.

XS
SM
MD
LG