Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara wa'adin Jefa Kuri'u A Kasar Georgia - 2003-11-03


Jami'ai a tsohuwar jamhuriyar Tarayyar Soviet ta Georgia sun kara tsawon wa'adin jefa kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin jiya lahadi a bayan da jama'a suka bayyana fuskantar matsaloli.

An rufe rumfunan zabe a wasu sassan kasar, ko kuma sun fuskanci karancin takardun kuri'u, yayin da aka rufe wasu kafin cikar wa'adi. Wasu 'yan kasar ta Georgia sun koka da cewa sun kasa jefa kuri'u a saboda babu sunayensu a kundin rajistar masu jefa kuri'a.

An tsawaita lokacin jefa kuri'a a Tbilisi, babban birnin kasar, da kuma a Kutaisi.

Wannan zabe na 'yan majalisar dokoki su 235, yana iya zamowa ma'aunin gwajin farin jinin 'yan siyasar da zasu yi takarar kujerar shugabancin kasar a shekarar 2005. Kuri'un neman ra'ayoyi na baya-bayan nan sun bai wa jam'iyyar "For-A-New-Georgia" mai goyon bayan gwamnatin kasar goyon bayan kashi 6 ne kacal daga cikin 100 na masu jefa kuri'a, kasa sosai da irin goyon bayan da jam'iyyun adawa ke samu.

XS
SM
MD
LG