Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ji Rauni Wa Mutane Hudu A Fashe-Fashen Nakiyoyi Jiya Talata A Iraqi - 2003-11-05


Jami'an sojan Amurka sun ce mutane hudu sun ji rauni a hare-haren da aka kai da makamai masu cilla kwanson nakiya a cikin yankin da Amurka ta kafa hedkwatarta a birnin Bagadaza.

An kai hare-haren na jiya talata a cikin yankin nan da ake kira "Koren Yanki" a turance a birnin na Bagadaza, watau a inda rundunar sojojin Amuirka da ma'aikatan hukumar taron dangi suke kwana tare da aiki.

Ba a fahimci ko wadanda suka ji raunin sojoji ne ko kuma fararen hula ba.

Tun da fari a jiya talatar, an kashe sojan Amurka daya, aka raunata wasu guda biyu a lokacin da wani bam da aka dasa a gefen hanya ya tashi a Bagadaza. A jiya talatar, shugaba Bush ya ce kashe sojojin Amurka da ake yi bai karya wa Amurka guiwa game da ayyukan da take gudanarwa a kasar Iraqi ba.

XS
SM
MD
LG