Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare hakkin Bil Adama Ta Zargi Guinea Da Laifin Keta Takunkumin Makaman Da Aka Sanyawa Liberiya - 2003-11-05


Kungiyar "Human Rights Watch" ta zargi Guinea da laifin keta takunkumin makaman da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta sanyawa Liberiya ta hanyar samarwa da 'yan tawayen kasar makamai.

Kungiyar kare hakkin jama'ar mai hedkwata a New York, ta yi wannan zargi a cikin wani rahoton da ta bayar yau laraba.

Ta ce Guinea ta samarwa da kungiyar 'yan tawaye ta "Liberians United for Reconciliation and Democracy" makamai.

Har ila yau, kungiyar kare hakkin jama'ar ta ce a farmakin karshe da suka kai a watan yuli, 'yan tawayen sun yi ta harbin kan-mai-uwa-da-wabi da makaman da suka samu daga Guinea a kan yankunan fararen hula. An kashe mutane da dama, dubbai suka ji rauni a wannan farmakin.

Guinea ba ta mayar da martani ga zargin ba, amma kuma a can baya ta musanta cewa akwai wata hulda tsakaninta da 'ya tawayen.

MDD ta sanyawa Liberiya takunkumi a saboda rawar da ta taka a yakin basasar Saliyo.

XS
SM
MD
LG