Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canada Tana Kokarin Kafa Dokar Samar Da Magunguna Masu Araha Ga Kasashe Matalauta - 2003-11-05


Canada zata gabatar ad wata sabuwar doka wadda aka tsara da nufin sayarwa da kasashe matalauta magunguna masu arha sosai domin yakar cutar kanjamau da wasu cututtukan.

Firayim minista Jean Chretien ya fada a Ottawa, babban birnin Canada, cewar a cikin makon nan za a gabatarwa da majalisar dokoki wannan kudurin doka ta sauya dokokin da suka shafi magunguna da kare abubuwan da wani ya kirkiro daga masu yin kofe.

Yayi wannan furucin ne kuwa a wajen taron 'yan jarida na hadin guiwa da suka yi tare da shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu mai ziyara a kasar.

Firayim ministan na Canada ya ce sabuwar dokar zata aiwatar da wata yarjejeniyar da Kungiyar Cinikayya ta Duniya ta cimma kwanakin baya kan bai wa kasashe matalauta damar sayen kofen magunguna masu rahusa daga kasashen waje.

Har ila yau, ya ce kasar Canada zata zamo kasar farko a duniya da za ta gabatar, tare da yin muhawara a kan irin wannan doka.

Shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu ya ce ya gamsu sosai da wannan sanarwa ta firayim ministan na Canada.

XS
SM
MD
LG