Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Saman Yakin Amurka Sun Jefa Bama-Bamai Kusa Da Garin Fallujah A Iraqi - 2003-11-10


Rundunar sojojin Amurka ta ce jioragen yaki sun jefa bama-bamai a wani yankin dake kusa da garin Fallujah na Iraqi, a bayan da aka kai hari kan sojojin Amurka a wannan wuri.

Jami'ai suka ce jiragen yaki sun jefa bama-bamai uku masu nauyin kilo 227 kowanne a kan wurin nan da aka harbo wani jirgin helkwaftan sufuri na sojojin Amurka a makon jiya har aka kashe sojoji 16.

A ranar asabar, wata nakiyar da ta tashi a gefen kwambar motocin soja a Fallujah ta kashe sojojin Amurka biyu ta raunata wani guda.

A halin da ake ciki, wani babban wakilin Majalisar Mulkin Iraqi, ya fada jiya lahadi cewar majalisar tasu zata fito da tsarin lokaci na rubuta sabon tsarin mulki nan da wa'adin ranar 15 ga watan Disamba da aka tsayar. Amma kuma ministan cikin gida na wucin gadi, Hoshiyar Zebari ya ce tabarbarewar al'amuran tsaro tana iya jinkirta rubuta sabon tsarin mulki, wanda za a zana da nufin share fagen gudanar da zabe.

XS
SM
MD
LG