Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattijan Amurka Ta Zartas Da Kudurin Kakabawa Syria Takunkumi - 2003-11-12


Majalisar dattijan Amurka ta amince da kafa sabon takunkumi kan kasar Syria saboda huldar da aka yi zargin wai tana da ita da kungiyoyin 'yan ta'adda, da kuma wani yunkurin da aka ce wai tan ayi na mallakar haramtattun makaman kare-dangi.

A jiya talata majalisar dattijan ta zartas da wannan kuduri da kuri'u 89, inda wakilai 4 kawai suka jefa kuri'ar rashin yarda da matakin. A watan da ya shige ita ma majalisar wakilai ta Amurka ta zartas da irin wannan kuduri.

Kudurin dokar zai bai wa Amurka iznin sanyawa Syria takunkumin cinikayya da na tattalin arziki har sai lokacin da fadar White House ta ce Syria ta daina goyon bayan 'yan ta'adda.

Shugaba Bush ya jima yana yin adawa da irin wannan kuduri, amma kuma acikin 'yan kwanakin nan fadar White House ta nuna cewa zai rattaba hannu a kai.

XS
SM
MD
LG