Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obasanjo Zai Tattauna Da Mugabe A Birnin Harare - 2003-11-17


An shirya shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe zai gana da takwaransa na Nijeriya, shugaba Olusegun Obasanjo, yau litinin a Harare, domin tattauna taron kolin kungiyar Kwamanwels wanda ba a gayyaci Mr. Mugabe ba.

An dakatar da Zimbabwe daga cikin kungiyar ta Kwamanwels a watan Maris na 2002 a saboda keta hakkin bil Adama da kuma zargin cewa shugaba Mugabe yayi magudi a zaben shugaban kasar da aka ce ya sake lashewa a shekarar.

A cikin watan Satumba, kungiyar Kwamanwels mai wakilai 54, wadda ta kunshi Ingila da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka, ta bayar da sanarwar cewa dakatar da Zimbabwe da aka yi tana nufin cewa ba zata halarci taron kolin na watan Disamba wanda Nijeriya zata karbi bakunci ba.

Rahotannin kafofin labarai sun ce Nijeriya da Afirka ta Kudu sun bukaci kungiyar Kwamanwels da ta gayyaci Zimbabwe zuwa wurin wannan taron koli.

XS
SM
MD
LG