Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Shekarau na Jihar Kano zai kaddamar da riga kafin shan inna - 2004-07-29


Gwamna Shekarau na Jihar Kano zai kaddamar da riga kafin shan inna.

Gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim shekarau, zai kaddamar da allurar riga kafin shan inna a karamar hukumar Takai. Malam shekarau ya shirya zai je wurin tare da iyali sa da mataimakin sa da sarkin kano, mai martaba Alhaji Ado Bayero, inda a nan Gwamanan zai soma diga ma yaran sa biyu, 'yan kasa da shekarun biyar, sanadarin maganin domin kaddamar da allurar a duk fadin jihar. Zai yi wannan abun ne, a matsayin nuna kyakkyawan misali ga jama'a domin su tabbatar cewa maganin da a yanzu, aka amince ayi anfani da shi a jihar, ba ya da wata illa zuwa ga 'yaya mutane.

Bayane daga kwamitin riga kafin cututuka na jihar ya nuna cewa, an tsara kwamishinoni da masu bada shawara da manyan sakatarori da jiga jigan gwamnati da na jam'iyar mai mulki, duk zasu tafi yankunan su inda zasu bayar da yaran su ayi musu riga kafin, don ba jama'a tabbacin maganin ba ya da wata illa ga al-ummar jihar. An sa ran za'a yi wa yara sama da milyan hudu riga kafin a cikin kwanaki hudu da za'a yi ana allurar.

XS
SM
MD
LG