Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan da Indiya sun kammala wata tattaunawa kan batun da ya shafi ta'addanci - 2004-08-11


Yau laraba Indiya da Pakistan su kammala wata tattaunawar kwanaki biyun da su ka yi a Islamabad, baban birnin Pakistan, inda suka siffanta ta da cewa tattaunawa ce mai ma’ana ba kuma tare da inda-inda ba.

A cikin ita wannan tattaunawar da ta shafi batutuwan ta’ddanci da kuma shige da ficen miyagun kwayoyi masu sa maye, mashawartan kasashen guda biyu basu bada cikakken bayanin dukanin abubuwan da su ka zanta ba, illa dai kawai cewa akwai kudurin ci gaba da yi shawarwari tsakaninsu.

Ita dai wannan tattaunawa tana da ga cikin ire-iren musayar ra’ayoyin da mahukuntan tsaka-tsaki na kasahsen ke ta yi ne kafin taron da ake sa ran ministocin harkokin wajensu zasu gudanar cikin watan gobe a New Delhi, idan Allay ya kaimu.

Kasahen India da Pakistan, wanda dukkaninsu su na da makaman nukiliya sun gwabza a wasu manya-manyan yake-yake guda uku da kuma kanan masu yawan gaske, tun lokacin da su ka sami ‘yancin mulkin kansu daga Ingila a shekarar 1947. Duk kuwa rikece-riken na su sun ta’allakane kan makomar lardin Kashmir wanda kasahen biyu suka tsaga gida biyu, kuma kowaccensu ta mamaye bangare guda daga ciki.

Ita dai gwamantin Indiya ta na zargin gwamnatin Pakistan da kasancewa ummul-khba’isin ta’addancin da ke gudana a bangarorin da Musulmi su ka fi yawa na Kashmir din, wanda kuma su ke karkasin mulkin Indiyan.

Sai dai Pakistan din ta musanta dukkanin zarge-zargen, ta kuma ce duk yawancin mutanen da Indiyan ke kira ‘yan ta’dda, alal hakika, mutane ma su neman ganin cewa Kashmir da al’ummarta sami ‘yancin kansu ne kawai.

Amma wani mai fashin bakin siyasa a Pakistan mai suna Ayaz Amir ya ce gwamnatin ta Pakisatan ta dan sassauta matsayinta game da wannan batu tun lokacin da aka fara sabuwar tattaunawar batun kawo zaman lafiya a bara, inda ta yarda kan zata taka rawar azo-a-gani wajen hana mayakan gwagwarmaya samun mafaka bangaren Kashmir din dake karkashinta.

Ya ce, “Pakistan ta yi matukar watsi da matsayinta kan wannan al’mari, sakamakon irin matsin-lambar da Amurka ke mata da kuma wasu abubuwa makamantan hakan”. Ya kara da cewa, ya na kyautata zaton hatta ita wannan zantawar da ake a halin yanzu, ba zau yiwu a ci gaba da ita ba, idan da Pakistan din ba ta yarda da murkushe irin kunnokan da ‘yan gwagwarmayar ke yi ba daga kan iyakar ita Kashmir din da Pakistan.

Har ila yau, Mr.Amir na ganin cewa, goyon bayan da Pakistan ke bayarwa ga kokarin ganin Kashmir ta sami mulkin gashin kanta matsayi kawai take bayyanawa, amma ba manufarta kenan ba. Saboda haka, ya ce “Wannan dai kawai suna yi ne domin su fadi albarkacin bakinsu da kuma matsayinsu”.

Sabili da wannan ne Mr. Amir ya ke ganin ita wannan tattainawa da aka kammala ba wata aba bace illa shaukatun-bangaro kawai

XS
SM
MD
LG