Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojin Iz'raila sun kashe Palasdinawa 'yan gwagwarmaya a zirin Gaza - 2004-08-17


Sojin Izra'ila sun kashe Palasdinawa biyu masu gwagwarmaya a kusa da wani matsugunnin dake zirin gaza. sojin Izra'ilar sun ce an kashe mutanen ne bayan an gane su dauke da wasu ababe da akayi imanin na tada nakiyoyi ne. Lamarin ya auku ne a kusa da wani matsugunnin yahudawa a garin Gaza.

Wata kungiyar Abu el-Reesh dake da alaka da reshen kungiyar Fatah ta shugaban hukumar palasdinawa Yasser Arafat, ta bada sanarwar kashe wasu 'yankungiyar su biyu. Kungiyar ta fada a cikin sanarwar da ta bayar cewa, an kashe mutanen biyu ne 'yan garin Khan Younis, wanda ke a birnin Gaza a lokacin da suke dana wani bom a gefen wata motar jeep ta sojoji.

Ranar litinin, helikwabtar yakin Izra'ila ya kashe wasu mutane biyu a lokacin wani farmaki a garin Beit Hanoun na birnin Gaza. Sojin sun ce, mutanen na kokarin, halba wasu rokoki zuwa Izra'ila ne.

A karkashin wani shirin Priministan Izra'ila Ariel sharon wanda ke cike da rudani, za'a rushe duk matsugunnen yahudawa da wasu hudu dake gabar yamma na kogin jordan. Wannan yunkuri ya jawo rashin kwanciyar hankali a Gaza domin kuwa bangarori da dama su na ta gwagwarmayar neman ikon don cika gurbin da ake sa ran hakan zai haddasa.

A wata kuma, ma'aikatar kula da gidaje ta Izra'ila ta buga wani jirin gidaje guda dubu da za'a gina a matsugunnai hudu wandanda ke gabar yamma na kogin jordan. wannan yunkurin dai ya fusata jam'iyar masu adawa ta laiba, wadda ke tattaunawa domin yuwuwar shiga cikin gwamnatin Mr sharon.

XS
SM
MD
LG