Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arafat ya yi alkawalin yin gyara ga hukumar palasdinawa - 2004-08-19


Arafat ya yi alkawalin yin gyara ga hukumar palasdinawa:

Shugaban palasadinawa Yasser Arafat ya amsa cewa an tabka kurakurai a hukumar mulkin palasdinawa. ya kuma dauki alwashin gyara kurakuran. A wani jawabin ga 'yan majalisar dokokin palasadinawa a garin Ramallah na yammacin kogin jordan, Mr Arafat ya ce wasu jami'an sa ba shakka sun yi kurakuran da basu dace ba, tare kuma da amfani da mukaman su ta hanya maras kyau. Ya ci gaba da cewa "akwai matakan da basu dace ba da wasu hukumomi suka dauka, wadanda daga cikin su wasu na rashin mutunci ne, da aka yi amfani da mukamai ta hanyar banza," ya kara da cewa " ba wanda ya wuce yi kuskure, daga shi har sauran makaraban sa". Sai dai Mr Arafat bai ambaci sunan kowa ba, bai kuma bada bayani dala-dala ba na irin kurakurai da musgunawar da aka yi. Wannan shi ne kallamin da yafi fitowa karara a fili tun bayan da tashin hankali ya barke a zirin gaza a cikin watan yulin da ta wuce. A karo na farko kenan da shugaban palasdinawan ya amsa cewa shi da kan sa ma ya tabka kurakurai. Mr Arafat ya yarda cewa an kasa wanzar da doka da oda a yammacin kogin jordan da zirin gaza. Ya kuma bada tabbacin bada goyon baya domin kyautata yanayin. Ya ce " mu na bukatar tafiya tare da zummar aiwatar da gyara da kawo sauye-sauye akan kurakuran. Bai dai fadi irin matakan da za'a dauka ba. Mr Arafat dai ya na shan suka daga kasashen duniya akan kasawar sa na gudanar da sauye-sauye a hukumar palasdinawa, musamman ma a hukumomin tsaron da ake ganin sun kasa tabuka komi, ga shi kuma cin hanci da rashawa ya dabaibiye su. Mai yuwa suka mafi tsanani da ya ake yi ma sa ya fi fitowa ne daga al-ummar sa ta palasdinawa.

XS
SM
MD
LG