Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lamarin Darfur ya zarce abun da Gwamnatin Sudan ke cewa - 2004-08-19


Lamarin Darfur ya zarce abun da Gwamnatin Sudan ke cewa: Wani kudurin kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya ba kasar Sudan wa'adin har zuwa karshen wannan watan na ta kawo karshen tashin hankali a yammacin Darfur, ko kuma ta fuskanci ladabtarwa ta fanin tattalin arziki da na diflomaciya. Kwararru a wajen wata tattaunawa da Jami'ar Johns Hopkins ta dauki nauyi shi sun ce muni lamarin Darfur ya wuce abun da Gwamnatin Sudan ta ke fada.

Yake - yake a yankin Durfur tsakanin 'yan tawaye da mayakan sai kai da gwamnatin ke mara wa baya, wadanda aka sani da sunan Janjeweed, tuni ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatar farar fula, yayin da mutane sama da milyan guda suka rasa muhalin su. Kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya ya amince da kudurin akan yankin Darfur ne a karshen watan jiya. A daidai lokacin ne kuma, wakilin majalisar dinkin duniya na mutanen da suka rasa matsugunnin su, Francis Deng ya ziyarci kasar ta sudan. Ya ce mahukumta a Khartoum da kuma Darfur sun gaya muna cewa lamarin tsaro ya kyautatu, kuma wannan ya ba mutane kwarin gwiwa na komawa can. ya ci gaba da cewa " a gaskiya ma, cewa sukayi mutane na ta komawa bisa ratin kansu domin ba wata matsala a kyauyukan su. " Mr Deng ya ce sai shi wadanda ya zanta da su,wadanda suka rasa muhalin su,a gaskiya abun da suka sheda ma sa ya sha banban gameda ainihin lamarin da bai wani sauya wa ba. Ya kara da cewa " Mutane sun ce har yanzu akwai rashin tsaro" " yayin da sansanonin ke da kwanciyar hankali, fita daga cikin su ya na sa mutum ya fuskanci hadarin akai ma sa hari ko ma a kashe sa ko kuma ayi ma mata fyade. Wannan dai ya sa jama'a da dama yin dari-darin komawa kyauyukan su. Kodayake, a zahiri su kan bayana shawar son komawar, amma suna tunanin har yanzu akwai hatsin yin hakan. John Prendergast na wata kungiyar sasanta rikici ta duniya ya ce Gwamnatin Sudan din ta janye duk wata cikas da ke hana ma kungiyoyin sai kai da bana gwamnati ba aiwatar da ayukan su a yankin Darfur. Sai kuma ya ce ci gaban rikici shi ne babban matsalar da ke hana kungiyoyin duniya gudanar ayukan su na agaji. Mr Prendergast ya kara da cewa ko da ma fadan ya lafa, yawan barkewar cututuka kamar wadanda uka jibanci ruwan sha da makamantan su, zasu cigaba da halaka mutane.

XS
SM
MD
LG