Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An soma shawarwarin zaman lafiya akan Sudan - 2004-08-23


Jami'an gwamnatin Sudan da shugabannin kungiyoyi biyu na 'yan tawaye sun soma shawarwarin kawo karshen tashin hankali a yankin Darfur na yammacin a Abuja, babban birnin Najeriya. Kawo yanzu gwamnatin sudan ta ki ta amince da sharuddan da 'yan tawayen suka gintaya mata a karshen wani taron da aka yi a watan juli. An Shawarwarin na yanzu ne mako guda kafin cikar wa'adin da majalisar dinkin duniya ta ba kasar ta Sudan na ta kawo karshen tashin hankali a yankin Darfur. Farar fula sama da miyan guda ne suka rasa matsugunnin su ko kuma suka tsere don guje ma yaki a tsakanin 'yan tawaye da kuma mayakan sa kai na larabawa da gwamnatin ke marawa baya wadanda ake kira, Janjaweed. kakakin shugaba Obasanjo na Najeriya, Mrs Remi Oyo ta ce ta na sa ran shawarwarin da ake yi a Abuja zasu kai ga samar da zaman lafiya a kasar Sudan. A cewar ta " ina jin akwai mahimmin bukatar a basu dama. Ba wani mahalukin da baya muradin zaman lafiya, kuma mun yi imanin a nan Najeriya a karkashin shugaban Obasanjo dukkan wadanda ke da hannu a lamarin na Sudan da ma cikakkun 'yan Afirka na gari zasu so su ga wannan shawarwarin sun yi nasara. Mu na kuma kyautata zaton zasu yi nasara. Kakakin shugaba Obasanjon ta ce an gayaci shugabannin manyan kungiyoyin 'yan tawayen biyu, watau na sudan liberation army da na justice and equality movement da wakilan gwamnatin Sudan da kuma shugabannin kasashen Chadi da libya, zuwa wajen shawarwarin. Ta kuma ce Najeriya a shirye ta ke ta ci gaba da daukar nauyin shawarwarin sai an cimma yarjejeniya. A jiya lahadi shugaba Obasanjon na Najeriya, wanda kuma shine har wa yau shugaban kungiyar tarayar Afirka, ya fito a gidan talabijin na kasar inda ya nuna bukatar kungiyar tarayar Afirka na taka wata muhimmiyar rawa a kasar Sudan. Ya ce rundunar tarayar Afirka zasu kwance wa 'yan tawayen damara yayin da ita kuma gwamnatin Sudan ta dauki nauyi kwance damarar mayaka 'yan sa kai na Janjeweed domin kawo karshen yakin. Ministan harkokin wajen Britaniya Jack Straw, tuni dai ya bar london zuwa kasar Sudan, inda zai tattauna rikicin na Darfur da shugaba Omar al- Beshir da manyan jami'an gwamnatin shi.

XS
SM
MD
LG