Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha na bincikar hatsarin jiragenta biyu - 2004-08-25


Masu bincike a Rasha na binciken dalilan da suka jawo hatsarin jiragen saman fasinja biyu wadanda suka fadi a lokaci guda alokacin da suke tafiya daga Moscow zuwa wasu birane a kudancin kasar.Mutane tamanin da tara ne suka halaka a wadannan hatsura biyu da suka auku da daddare. Ma'aikatan ceto na ci gaba da bincike a cikin tarkacen jiragen a wuraren da suka fado bayan da suka bace daga hangen na'urar hango jirage a lokaci guda. Karamin jirgin kirar Tupolev-134 ya fado ne a yankin Tula misalin kilomita dari da tamanin a kudancin Moscow a kan hanyarsa ta zuwa Volgograd. Shi kuwa daya jirgin, kirar Tupolev 154 ya fado ne a yankin Rostov-on-Don can a kudu kusa da tekun Black Sea. Wannan hatsarurruka biyu a lokaci guda ya jawo zargin cewa su dai jiragen an yi fashinsu ne ko kuma an sanya musu bamabamai ne wanda yayi sanadiyar fadowarsu. Akwai dai rahotanni wanda ba a tabbatar da su ba wanda ke cewa babban jirgin ya aika da sakon gaggawa kafin ya fado. Bayan da ya samu labarin wannan hatsarin, shugaba Vladamir Putin ya sanya hukumar tsaron cikin gida ta FSB da ta binciki aukuwar hatsarin. Jam'ian FSB sunce har izuwa yanzu basu samu wata cikakkiyar shaida data nuna cewa akwai hannun 'yan ta'adda a wannan hatsarin jirage ba. Sunce matsalar injina ko rashin bin ka'idoji ka iya kasancewa dalilan wannan hatsari. Mai bincike Gennady Skachkov yace tarkacen jirgi a daya daga cikin wuraren hatsarin ya nuna alamar cewa babu maganar fashewar wani abu. Yace jirgin yana hade kuma tarkacensa bai warwatse ba.Ya kuma kara da cewa jirgin bai aika da wani sakon gaggawa ba. 'Saboda haka bamu gane yadda hatsarin ya auku ba'. Su dai jiragen sun tashi ne da tsirar awa daya daga filin jirgin saman Domodeyevo a Moscow daya daga cikin filaye biyar na kasuwanci.Kuma filin na daya daga cikin na zamani a Rasha kuma yana da kayayyakin kula da tsaro. Amma akwai matukar damuwar harkokin tsaro a Rasha saboda yakin da ake fama da shi a ballallen yankin Checheniya a inda sojojin Rasha ke yaki da mayaka na 'yan aware masu son ballewa tun kusan shekaru goma da suka wuce. An sha samun fashewar bamabamai a Moscow da wasu birane a 'yan shekarunnan wanda kuma ake dangantawa da yan Checheniya.A lahadi mai zuwa ne za'a gudanar da zabe a Checheniya don maye tsohon shugaban yankin wanda 'yan awaren suka kashe ta hanyar bam a watan Mayu. Shahararren dan siyasar Checheniya,Aslan Maskhdov ya nisanta kansa daga wannan hatsarin jirage.

XS
SM
MD
LG