Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Republicans sun bude babban taronsu a New York - 2004-08-30


A ranar litininne aka bude babban taron jam'iyyar republican a New York a inda za a gabatar da shugaba Bush a matsayin dan takarar shugaban kasa domin samun amar ci gaba da shugabancin kasa na wasu tsawon shekaru hudu masu zuwa.

'Yan Republican sun zabi New York, inda jami'yyar democrat ke da karfi ne ba dadewa da kai harin ta'addanci na sha daya ga watan Satumba na shekara ta dubu biyu da daya kan cibiyar kasuwanci ta duniya da kuma hedikwatar tsaro ta Pentagon. Matakin kai hari ga kungiyoyin al-Qaida dana abokansu yan Taliban ya jawo farin jinin shugaban ya ragu.

Amma a lokacin da dubannin 'yan zanga-zanga suka hau kan tituna ranar lahadi don nuna rashin amincewarsu da shiga yaki da Iraqi da kuma sauran matakai kan sauran abubuwa, mataimakinsa Dick Chiney a lokacin kamfen a New York, ya tunawa Amirkawa dalilinsu na yin babban taron jam'iyyarsu a New York.'Shi mutumne mai cika alkawari kamar yadda 'yan Taliban suka fara gani.A karkashin shugabancinsa mun koresu daga mulki a Afghanistan kuma muka rufe sansanonin da ake horar da 'yan ta'adda su kashe Amirkawa' yace.

A kokarin ganin an jawo hankalin masu jefa kuri'a wanda basu karkata ga kowa ba, babban tarron zai yi kokarin gabatar da 'yan jam'iyyar masu matsakaitan ra'ayi.Daga cikin masu jawabi a ranar litinin akwai dan majalisar dattijai John McCain daga Arizona da tsohon kwamishinan 'yan sandan birnin New York, Bernard Kerik wanda ya horar da 'yan sandan Iraqi a bara.

Jam'iyyar Republican tana fatan ta samu karbuwa ta hanyar ba dan democrat, dan majalisar dattijai Zell Miller daga Georgia dama yayi jawabin bude taron a wani lokaci cikin wannan makon.

Dan majalisar dattijai Miller ya dan fadi wani bangaren jawabin da zai gabatar ga FoxNews ranar lahadi a inda ya yabawa shugaba Bush. 'Ina ga yana da manufa mai kyau ga wannan kasa kuma ina ga zai bayyana wannan manufa a daren ranar Alhamis. Ina tunanin cewa ya san inda yake so ya kai kasarnan, aganina ya kamata mu mara masa baya domin ya kaimu inda yake so ya kaimu', yace.

Shi kuwa tsohon shugaban kasa Bill Clinton wanda mazaunin New York ne kuma ya kasance yana da ofishi a wannan birnin cewa yayi bawa masu matsanantan ra'ayi mahimmanci a taron baya nuna a zahiri tsattsauran ra'ayin ginshikan jam'iyyar. Yayi wannan kalaman nasa ne a lokacin taya cocin Riverside murna a inda yace 'manufofinsu na hana zubar da ciki ne da yaki da 'yancin 'yan luwadi da kuma tara dukiya da mulki'. Shugaba Bush ba zai isa wurin wannan babban taro ba sai ranar laraba dab da lokacin da zai amince da tasayar da shi takara da jam'iyyarsa tayi.

XS
SM
MD
LG