Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau ne shugaba Bush zai bayana a gaban 'yan jam'iyar sa ta Republican - 2004-09-02


Yau ne ake sa ran shugaba Bush zai bayana a gaban 'yan jam'iyar sa ta Republican da ma kasar bakin daya domin amincewa da tsayar da shi dantakarar shugaban kasa na jam'iyar a karo na biyu. Jawabin na sa kamar irin wanda John Kerry na Jam'iyar Damokatar ya yi, wata daya da ya gabata a Boston, za'a sa ido akan sa so sai. Sai dai, jawabin zai zama na daban ne.

A lokacin da John kerry ya yi jawabi ga babban taro na Jam'iyar Damokarat, ya yi ta da wata manufa na wani takamaiman abu a ran sa, inda ya ke cewa " Ni ne John Kerry, na zo in kama aiki."

Babbar manufar sa a lokacin ita ce na ya gabatar da kan sa ga Jama'ar Amerika, bayan ya shafe watanni ya na mayar da hankalin sa akan yadda zai samu goyon bayan 'yan Jam'iyar sa. A shekara ta 2000, George Bush, wanda shi ne Gwamnan Texas, shi ma ya fuskanci irin wannan lokacin da ya yi wa babban taron Jam'iyar sa ta Republican a Philadelphia.

Ya ce " Na taba zaman inda ni ke da alhakin komai a kasuwanci da ma gwamnati. Na taba zama shugaba wanda ke tsara ajenda da manyan kudurori, sa'annan in nemi mutane su yarda dasu su kuma aikata su a samu nasara" . A wannan lokacin dai Shugaba Bush, zai yi jawabi a matsayin sa na shugaban kasa mai ci. Babban aikin sa ba wai ya gabatar da kan sa ba ne a'a, zai dai fayace irin ababen da ya yi a lokacin wa;adin sa na farko, sa'annan ya kuma gabatar da hujjojin da zai sa ya sake komawa kan karagar mulki.

Dan majalisar dattawa na Ohio Mike DeWine zai kasance a sahun gaba a wajen babban taron. Ya kuma ce da ma mutanen Amerika sun riga sun san George Bush. Ya ce " sun san shi. sun kuma san sosai. Ina zaton a lokacin jawabin godiya na amincewa da tsayar da shin jama'a zasu so su ji " me zaka sake yi muna...ina zaka kai kasar nan a cikin shekaru hudu masu zuwa." Ya yi hasashen Mr Bush zai gabatar da jawabi mai kama biyu, watau rabi na kampe, rabi kuma rahoton ayukan sa ga jama'ar kasar. Zai nuna irin nasarorin da ya samu tare da fayace shirin abun da zai a gaba. Wata wakiliya daga jihar California Linda Dealy ta ce Mr Bush ba zai fuskanci wata adawa ba, amma dai jawabin sa na godiyar ya amince na da mahimmancin gaske. Jawabin godiya na amincewa shi ne daya daga cikin damar da wanda ya ke dan takarar shugaban kasa zai samu a lokacin zabe inda zai yi jawabi a manyan kafafen labarai a kasar amurka ba tare da an katse sa ba ko ma a dakatar da jawabin. Akan bada irin wannan damar a lokacin da ake mahawara a gidajen talabijin na kasa.

XS
SM
MD
LG