Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Sudan sun ce matsa lamba daga kasashen waje na iya ... - 2004-09-09


Wani babban jami'in gwamnatin Sudan, yace matsin lamaba daga kasashen waje na a samar da zaman lafiya a yankin Durfur da yaki ya kachachala na iya durkushewa. Mataimakin kakakin majalisar dokokin sudan, Angelo Beda ya sheda ma manema labarai a Nairobi, babban birnin Kenya, cewa yunkurin Amurka na son bayana lamarin Darfur a matsayin kisan "kiyashi" ne da kuma barazanar sawa Sudan takunkumi da Majalisar dinkin duniya tayi na iya sa a samu cikas a kokarin samu sulhu a tsakanin gwamnatin da 'yantawaye.

Mr Beda, yace maganar kisan kiyashi da zancen sa takunkumin yana bada abun da ya kira" wata alama maras ma'ana ga 'yantawaye da mayaka 'yan sa kai dake fafatawa a yankin na Darfur. A cewar kungiyoyin kare hakin bil-adama, mayaka 'yan sa kai da gwamnati ke marawa,watau 'yan Janjaweed sun na nan suna ta kai ma al-ummar bakar fata hari sannu alaikum,kodayake gwamnatin Sudan ta musanta wannan zargin.

Ana ci gaba da shawarwarin samar da sulhu tsakannin gwamnati da 'yantawayen a abuja,babban birnin tarayar Najeriya, sai dai kuma an ce tattaunawar na dab da durkushewa.Yanzu haka dai kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya yana shirye-shiryen zama domin,yin nazari akan ko gwamnatin Sudan ta cika alkawalin kwance damarar 'yanjanjaweed, da ko ta samar da tsaro ga mutanen dake zaune a Darfur, da kuma ko lalle ta na barin kayan agaji na kai ga fararen fular yankin.

Da dama dai, majalisar dinkin duniya ta ba gwamnatin Sudan, wa'adin zuwa karshen watan agusta na ta cika duk wadannan ka'idoji ko kuma, ta fuskanci wasu jirin takumkumin da bata ayana ba. A ranar laraba ne gwamnatin Amurka ta gabatar da wani dabtarin kuduri ga majalisar dinkin duniya inda tayi barazanar, sama sudan takumkumi akan man fetur muddin bata kawo karshen taka haken bil-adama ba, sa'annan ta kyale a tura sojin kiyaye zaman lafiya na tarayar Afirka masu yawa zuwa yankin Darfur. Mr beda yace yana da karfin gwiwar cewa majalisar dinkin duniya bazata sawa kasar sa takumkumi ba.

XS
SM
MD
LG