'Yansandan Indonesia sun tura karin jami'an tsaro zuwa wasu daga cikin ofisoshin jakadanci dake babban birnin kasar, Jakarta bayan da wani bom da aka dasa a wata mota a harabar ofishin jakadancin kasar Australia ya kashe mutum tara ya kuma jikkita wasu dari da tamanin.
Jami'ai suka ce babu wata sabuwar barazanar kai wani harin amma sunce an kara yawan ma'aikatan tsaro a ofisohin jakadancin Amurka , Japan da Australia. A can Australia, firaminista John Howard a ranar Jumma'a yace sake kai wani hari a Jakarta abinda zai iya abkuwa ne.
'Yan sanda sun ce sun yi imani wasu 'yan kunan bakin wake guda biyu ne suka kai wancan harin. Suka ce sun ajiye wata karamar motar daukan kaya makare da abubuwa masu fashewa a wajen harabar ofishin jakadancin Australia. Wani dandali a internet wanda aka sanshi da daukar ra'ayoyin Islama masu tsauri ya bayyana cewa wata kungiya mai alaka da al-Qaida, Jama'ah Islamiyah itace ke da alhakin kai wannan hari. Amma har yanzu ba a tabbatar da ingancin wannan ikirari ba.