Amurka ta nemi kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya bada izini a kaddamar da binciken kisan kare dangi da ake cewa an yi a kasar Sudan. Wani dabtarin kudurin da Amurka ta gabatar a gaban majalisar dinkin duniyar ya yi barazanar garkamawa Sudan takunkumin hana sayar da man ta idan har gwamnatin Sudan bata kawo karshen aika-aikar da ake yi a yankin Darfur ba. Wannan matakin dai yana fuskantar adawa.
Jekadun Amurka sun gabatar da dabtarin kudurin a wani kebabben taron kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya. Yunkurin ya zo sa'oi kalilan bayan sakataren harkokin wajen Colin Powell ya bayyana cewa an tabbatar da kisan kare dangi ya auku a yankin Darfur.
Bayan taron, jekadan Amurka a majalisar dinkin duniyar John Danforth ya yarda cewa akwai bukatar yin gyara ga dabtarin kudurin domin ya kumshi ababen da wasu kasashen dake kwamitin sulhun ke adawa dasu. Sai dai ya yi sha alwashin cewa ba za'a cire wasu ababen masu rudu da suka hada da, saka takunkumin sayar da man sudan ba. Yace "ba wanda zai sa takunkumi haka kawai don shawar yin hakan, a'i kuwa wannan abun mamaki ne". Ya ci gaba da cewa,"Akwai bukatar gwamnatin Sudan ta yi abun da ya dace domin ceton rayukan jama'ar, idan har kuma basu yi wani abun ba, suka ci gaba da yi jan lokaci, tau fa akwai yiwuwar daukar matakin da zasu dandana".
Jekadan China a majalisar , Wang Guangya, ya nuna adawa sosai da wasu ababen da aka sanya a cikin dabtarin, wanda ya hada da kiran, a kafa hukumar kasa da kasa domin ta yanke hukumci akan zargin kisan kare dangin. Yace China zata hau kujerar naki muddin ba'a a yi gyara ga dabtarin ba. Yace ba za mu amince da yadda dabtarin kudurin yake ba a yanzu.
Shi kuma jekadan Amurkan John Danforth, ya mayar da martani mai zafi game da shawar hawan kujerar naki. inda yake cewa kowane daga cikin kasashe biyar dake da damar amfani da damar ta su suna iya yin hakan, amma kuma su sani cewa tilas ne suyi bayani akan kazamin lamarin na Darfur. Ni ba zan iya yin bayani a madadin su ba, inji shi. Yace idan har akwai wani wanda ke son ya dauki nauyin ya zura ido, mutane su cigaba da mutuwa ana amfani da helikwabtocin yaki ana kashe su ana yiwa mata fyade, sai mun gani. Ban ga yadda wani zai iya bayana irin wannan lamarin ba.
Dabtarin kudurin na da goyon baya sosai. Britaniya da Faransa sun rattaba masa hannu a matsayin kasashe biyu dake gabatar dashi ta hadin gwiwa. Amma sai dai akwai akalla kasashe ukku na Pakistan da Rasha da Algeria da suka shiga sahun China wajen nuna adawa da kudurin.