Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojin Amurka ta kai farmaki - 2004-09-13


Rundunar sojin Amurka ta kai farmaki ta sama akan wuraren da ake zaton masu bore yantawaye sun mamaye a fallujah inda suka ja gada a can yammacin Bagadaza.Jami'an asibiti a can sun bayyana cewa mutane goma sha shidda ne aka kashe, yayin da wasu sama da goma sha biyu suka jikita a lokacin harin yau da safe.

Sojin Amurkan sun ce jiragen yaki da mayakan kasa su ne, suka kai abun da suka kira ' harin da ba kuskure' akan wani gini da kungiyar 'yanta'adda, wadda ke karkashin jagorancin da haifen jordan din nan Abu Musab al Zarqawi,ke gudanar da wani taron su. Jami'an sojin, sun ce harin ya biya bukatar da aka so, sai dai basu bada wani karin haske kan lamarin ba.

Wasu wadanda suka gannarwar idon su, sun ce sunji kara mai karfin gaske daga wasu ababe da suka fashe, suka kuma gan wani bakin hayaki yana tashi sama daga yankin al-shurta dake birnin, wurin da 'yan sunni suka fi gudanar da boren su.

Dama dai, Jami'an gwamnatin Iraqi sun bada sanarwar mutuwar mutane saba'in da biyar a fadan da akayi jiya lahadi, tsakannin rundunar sojin da Amurka take jagoranta da kuma masu bore a duk fadin kasar Iraqin.

XS
SM
MD
LG