Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron yaki da talauci na bukatar haraji kan kasashe  - 2004-09-22


Sugabannin Brazil da Faransa suna kira da a samar da haraji kan kasashen duniya don yakar talauci. An gabatar da shawarwarinne a lokacin taron kwana daya gabannin taron mahawara na shekara-shekara na babban taron majalisar dinkin duniya.

Shugaba Luis Inacio Lula da Silva na Brazil ne ya kira taron na shugabannin kasashe domin ya samar da wata hanya ta yaki da yunwa a duniya. Sama da shugabanni arba'in ne suke halarci taron mafi yawansu daga kasashe masu tasowa.

A jawabinsa ga taron, shugaban Brazil ya yi kira da a samu hanyoyin samar da kudade don yaki da talauci. "Muna nan domin samar da sabon babi a yaki da yunwa da talauci". Kada mu manta cewa yunwa itace babbar makami mai hatsari", ya ce.

Shugaba da Silva ya samu goyon bayan shugaban Faransa Jacques Chirac a shawarar sanya haraji kan kasashe domin gudanar da kamfe kan yaki da talauci. Jami'an diflomasiyya na Faransa da Brazil sunce harajin zai iya hadawa da na musayar kudade tsakanin kasashe da na tikitin shiga jiragen sama da na dakunan renon tsirai masu fitar da gas da kuma kan sayar da manyan makamai.

Shugaban Faransa, Chirac ya gayawa taron cewa ra'ayoyi da ake gani ba zasu karbu ba ko marasa ma'ana yanzu suna samun karbuwa, ya ce, 'yanzu camfi na bashi da wuri". "Muna sane da cewa a halin da ake tafiya yanzu babu alamar samum nasarar manunfofinmu. Sai mun nemi misalin dala biliyan hamsin a kowace shekara daga yanzu zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha biyar don cimma burinmu", ya ce.

Mista Chirac ya sauka a New York musamman domin taro kan talauci da hadewar kasashen duniya kuma yana son ya koma Faris da zarar an kammala taron. Komawarsa cikin gaggawa ya nuna cewa baza su hadu da shugaba Bush ba wanda ya isa New York ranar talata domin yin jawabi a bude mahawarar babban taron majalisar dinkin duniya. Gwamnatin Bush ta aika da mai matsakaicin mukami wurin taron, sakatariyar aikin gona Ann Veneman a matsayin wakiliya a wurin taron. A jawabinta Veneman ta yi maganganu masu zafi kan shawarar sanya haraji kan kasashe don shirye-shiryen yaki da talauci.

'An bawa sanya haraji kan kasashe mahimmanci don inganta arzikin wasu kasashe. Tace. "Haraji kan kasashe ba dimukuradiya bane, kuma aiwatar da shi ba zai yiwu ba.A jawabinsa tun da farko, sakataran majalisar dinkin duniya, Kofi Annan ya dauki matakin dan ba ruwanmu akan maganar haraji kan kasashen duniya domin yaki da talauci. Ya kara da cewa 'yana da sauki a ce a yi wani abu domin a samu a yaki talauci da yunwa. Kalubalen shine abinda za a yi.'

To amma mista Annan ya jawo hankalin cewa mahawara kan yadda za a yaki talauci kada ya zama hanyar hana cimma burin. Ya kuma lura cewa yawan masu fama da yunwa a duniya yana karuwa. Ya ce ya kamata a yi wani abu da gaggawa.

XS
SM
MD
LG