Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawarar Bush da Kerry - 2004-10-01


Magoya-bayan shugaba Bush da na sanata Kerry na da’awar nasu ne yayi nasarar muhawarar da aka yi.Ba tare da wata-wata ba, har an fara jin ta bakin masugudanar da yakin zabe na shugaba Bush da kuma na sanata Kerry kan muhawarar da ‘yan takarar shugaban-kasar suka yi a daren jiya Alhamis a can birnin Miami dake jihar Florida.

Magoya bayan shugaba Bush da na sanata Kerry, basu bata lokaci ba, a jiya Alhamis wajen fara kokarin gamsar da daruruwan manema labarai da suka hallara a inda aka yi muhawarar kan cewa dan takarasu ne yayi fice cikin muhawarar ta takarar zaben shekarar 2004.

Tun ma kafin a kammala ita muhawarar, sai suka fara bayyana irin wannan matsayi na su. Darektan kula da harkokin sadarwa na fadar White House Dan Barlett ya ce shugaba Bush ya nunawa Amurkawan dake da damar jefa-kuri’a cewa ya fahimci abubuwan dake damun daya dagacinsu kan tsoma-hannun da Amurka ta yi a kasar Iraki.

Yace, “Ni a ganina ya nuna fahimta gaske game da abubuwan da yaki ka iya haifarwa, haka kuma game da abubuwan da suka biyo baya kan hukuncin da ya yanke, ya kuma nuna dabarar da za’a bi domin yin nasarar yakin. Mr. Ballet ya kara da cewa, “Ina ganin daya daga cikin hujjojin da sanata Kerry ya kafa shine shugaba Bush bai fahimci hakikanin yadda abubuwa ke gudana ba ‘a Iraki, kuma ina ganin Bush ya nuna kuwa shine yafi kowa samun rahotanni game da hasarar-rayuwakan da ake a can”.

Shi kuwa sanata Bob Graham daga jihar Florida cewa yayi abokin aikinsa sanata Kerry ya gamsar da Amurkawa masu kada-kuri’a cewa suna da zabi ba kawai shugaba Bush ba. Ya kuma kara da cewa, “Da yawa da yawan Amurkawan da da suka yanke-sahawarar za su zabi Bush sun fasa hakan daga yau, suna kuma cewa, “Bari dai mu sake kananinmu na da game da John Kerry”. Wannnan zai sa ragowar muhawarure biyun da za’a yi kan batutuwan cikin-gida, wadanda kuwa mutanen Amurka na ganin shugaba Bush na da rauni a kansu, su zama masu muhimmancin gaske.

A yayinda dukkanin ‘yan-takarar biyu suka bamabanta da juna kan kudurin Amurka game da kasar Kuriya ta Arewa, da kuma alkawurran da amurka ta dauka kan yarjejeniyoyin kasa-da-kasa, da kuma kan ko wane irin matakai zasu dauka domin kawo karshen matsalar agaji a Darfur, amma dai halin da ake ciki a Iraki ne ya saha-kan dukkan sauran batutuwan a lokacin muhawar

XS
SM
MD
LG