Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bum din da ya tashi a pakistan ya kashe akallan mutane arba in - 2004-10-07


Wani bum da aka dana a cikin wata mota ya tashi a tsakiyar birnin Pakistan inda ya kashe mutane arba'in ya kuma raunata wasu da dama. An ce lamarin wani abun ne da ake jin gaba ce a tsakanin wasu musulmi wasu banbanicn dariku. Gwamantin ta ce zata sa soji su kare kasar daga yiwuwar afkuwar wani tashin hankalin a nan gaba.

Bum din ya tashi ne a lokacin wani taron dubban musulmi a yau a unguwar multan dake tsakiyar birnin pakistan. Wadanda suka gan abun, sun ce, bum din da ya tarwatse ya fada wa wasu gungun musulmi 'yan sunni dasuka shafe duk tsawon daren jiya suna bikin tunawa da shugaban su da aka kashe shekara daya da ta wuce.

Babban jami'in 'yansanda na yankin, Talat Mehmood Tariq ya sheda ma Muryar Amurka cewa, an tada bum din ne da wata na'ura ta hannu. A cewar sa, "Bayan an tashi daga taron kuma jama'a sun soma watse wa, akwai wata mota wacce yanzu haka mun samu burabutsan ta; an ji kuma kara mai karfin gaske na abun da ya fashe a cikin motar, wacce tayi fila-fila."

Mr tariq, wanda ya ce ana gudanar da bincike, yayi watsi da zargin cewa 'yan kunar bakin wake ne suka aikata lamarin. Ya ce zuwa yanzu dai, ba shedar da muka samu, kuma hakika ba gawar wani da aka samu a cikin motar. Wadanda suka gan afkuwar lamarin, sun ce nan take mutane ashirin da biyu suka sheka lahira. Likitoci a asibitocin Multan su na nan suna ta kokarin ceton rayukan mutane da dama. Ba dai wanda ya dauki alhakin kai harin bum din akan musulmin 'yan sunni.

Amma dai, wannan lamarin ya afku ne kwanakki shidda bayan wani dan kunar bakin wake ya kashe wasu masu ibada, 'yan shi'a marassa rinjaye, su talatin da daya a gabascin birnin sialkot.

Ana daura alhakin kisan shugabannin da mabiyan darikun biyu akan mabiyan su masu tsatsauran ra'ayi. Irin wannan tashin hankalin na 'yan darikun ya halaka daruruwan mutane.

XS
SM
MD
LG