Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahawaran Bush da Kerry - 2004-10-08


Shugaba Bush da abokin hamayar sa na jam'iyar Damokarat, John Kerry yau zasu gamu a wajen mahawara kashi na biyu inda zasu gwabza akan batutuwan da suka shafi lamuran cikin gida wato, abun da suka shafi jama'ar Amurka a gida.

Mahawarar da ta samo asili daga irin taron gargajiya don tattauna lamura a dandali, itace ginshikin Damokaradiyar Amurka. Lokacin Mahawarar su ta farko, wani dan jarida ne Jim Lehrer shi ne, ya jagorance ta ya kuma tsara duk tambayoyin da ya yi musu. Mutanen biyu dai sun tsaya a wurin da aka tanada batare da sunyi wa juna magana ba. Ba kamar ta farkon ba, wannan mahawarar ta yau a tsakanin su, itace ake kira dandalin shawarar mutanen gari. wannan irin dandalin ya samu karbuwa ainun a birnin New England kamin yakin juyin juya hali. Har yanzu ana cigaba da shi a wasu garuruwan.

'Yan gari sukan hadu a dandalin domin yin mahawara akan batutuwan da suka shafe su su kuma yanke shawara akan abun da ya damu al-ummar su. Profesa Loius wolfson yace abun da ake kira mahawara ta yakin neman shugabancin wacce ta ke kamar taron dandalin, ta yi kama da irin taron saduwa da manema labarai, amma dai kuma ta na da amfani.

XS
SM
MD
LG