Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwmnatin Kasar Afghanistan ta nemi a gaggauta bincike game da kura-kuran zabe - 2004-10-11


Hukumomin Afghanistan na sa-ran za’a kamalla bincike game da zargin tafka kura-kurai cikin zaben da aka gudanar a kasar. Ana fatan hakan zai samu, tun kafin a fito da sanarwar sakamakon zaben nan da zuwa wasu makonni.

Hukumar hadin-guiwar Majalisar Dinkin Duniya da Afghanistan mai gudanar da zaben shugaban kasar na farko, ta baiwa dukkanin ‘yan-takarar daka cikin zaben, wa’adin nan da ranar Talata mai zuwa, domin shigar da koke-kokensu game da zaben. Da yawa daga cikin ‘yan-takarar sun yi zargin cewar an tafka magudi lokacin da ake kada kuri’ar, duk kuwa da yunkurin da wasunsu suka yi na kauracewa zaben baki-daya.

Ray Kennedy, mataimakin shugaban ita hukumar zaben ya ce, yayi ammanar cewa, za’a kamalla binciken kafin a bada sanarwar sakamakon zaben. Amma yayi hamzarin cewa, jami’an zaben ba za su yi wani azarbabi kan batun ba. Ya kuma kara da cewa: “Muna son ganin an bada isasshen lokaci domin aiwatar da binciken. Domin kuwa yana da muhimmanci a tabbata komai ya tafi dai-dai.”

Za’a dauki makonni masu yawa kafin ‘a san dukkanin adadin kuri’un da aka kada, domin kuwa za’a kirga milyoyin kuri’un ne da hannu. Amma duk da haka za’a fara jin wani daga cikin sakamakon farko na zaben, nan da zuwa ‘yan kwanaki.

XS
SM
MD
LG