Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyun Amurka na fuskantar matsalolin zabe - 2004-10-29


A lokacin da Amurkawa ke shirin zaben shugaban kasa na gaba, manyan jam’iyyunsu guda biyu sun fara shirin tunkarar matsalolin zabe wadanda ka iya kunno kai a lokacin da kuma bayan zaben.

A cikin matakan da suka dauka jam’iyyun sun tura dubannin masu sa ido ‘yan jam’yyunsu zuwa tasoshin zabe a ranar zaben da kuma daukar dubannin lauyoyi wadanda za su yi shirin tunkarar matsalolin da ka iya tasowa. Jam’iyyun biyu suna nuna damuwa kan wannan zaben. A bangaren ‘yan Republican, babban abin damuwa shine matsalar rijistar zabe ta jabu.

Su kuwa ‘yan Democrat sun ce fitowar masu jefa kuri'a zai kasance ya amfane su sai kuma suka zargi ‘yan Republicans da kokarin hana kirga kuri’u na hakika. Shugaban Republican, Ed Gillespie ya gayawa gidan talabijin na NBC damuwarsu kan matsalar rijistar masu zabe wannan sun hada da kara yawan wadanda za su jefa kuri’a fiye da wadanda ya kamata su jefa kuri’ar da sunayen karya.

Don magance wannan matsalar tuni ita Republican ta dauki hayar dubannin ma’aikata wadanda za su kasance a tasohin zabe a mahimman jihohin Amurka a ranar zaben. 'Manufa shine a sa ido kan dubannin sababbin masu jefa kuri’a wadanda za su karbi takardun jefa kuri’a na wucin gadi saboda sunayensu ba sa cikin rijita. Yanzu wasu suna iya zuwa su yi rijista a wani wurin sannan su koma su jefa kuri’a a wurare uku ko hudu.'In ji Mista Gillespie. Ba zamu kirga wadannan kuri’un ba zamu tabbatar wannnan zaben na gaskiya ne. Takardun zabe na wucin gadi sun zama doka a duk kasar karkashin dokar zabe ta shekara ta dubu biyu da biyu wanda ya biyo bayan cece–kucen Florida bayan zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu

‘Yan Democrat na kalubalantar ‘yan Republicans kan damar yin zabe suna cewa wannan zai jawo tafiyar hawainiya sannan kuma ya hana wasu samun damar kada kuri’unsu. Shugaban Democrat, Terry McAliffe ya kuma zargi ‘yan Republicans da kokarin hana kirga kuri’u na halal. ‘ Burin Democrat shine a tabbatar an bawa duk wanda ya cancanta ya jefa kuri’a dammar da zai jefa kuri’arsa . Mun san ‘yan Republicans suna kokarin hana mutane dammar jefa kuri’unsu . Muna son kowa ya jefa kuri’arsa.’’ Jihar da za a fi fafatawa a zaben it ace Ohio wadda ke da masu jefa kuri’a kusan miliyan takwas. 'Muna da adadin wadanda aka yi wa rijista kwanannan mutum dubu dari shida da hamsin. Mun samu Karin masu jefa kuri’a,' in ji Dana Walch na ofishin sakataren cikin gida na Ohio.

Mista Walch ya ce tuni an kalubalanci sunaye dubu talatin kuma suna kokarin gano gaskiyar al’ amarin. Kimanin mutane miliyan dari da shida ne suka kada kuri’unsu a shekaru hudu da suka wuce kuma masana na hasashen karuwar masu kada kuri’a a wannan zaben. Akwai adadin sababbin masu jefa kuri’a kimanin miliyan goma zuwa goma sha biyar.

Abinda ya faru a zaben shekara ta dubu biyu ya sanya jam’iyyun biyu su kara shiri a wannan zaben. Wannan zaben na iya kasancewa zaben da zai fi fuskantar matsalolin shari’a a tarihin Amurka in ji kwararre kan al’amuran zabe Curtins Gans.

XS
SM
MD
LG