Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arafat ya bar Ramallah zuwa Paris don neman magani - 2004-11-01


Jagoran Palasdinawa Malam Yasser Arafat ya bar gidansa na Ramallah don neman maganin gaggawa a Faransa. Tarin mutane sun kasance suna daga masa hannu a lokacin da yake kokarin hawa jirgin sama mai saukar angulu mallakar sojojin saman Jordan a lokacin da yake barin gidansa na Ramallah.

Mota kirar limosin zagaye da jami’an tsaro da kuma manyan mataimakansa su suka rako Malam Arafat zuwa wajen jirgin saman wanda zai kai shi Amman. Mutane masu yawa ne suka cika wurin a lokacin da ya ke kokarin hawa jirgin. Amma wata kamarar talabijin ta samu damar dauko hoton fuskarsa a inda ya ke fara’a lokacin hawa jirgin.

Daga Amman zai hau wani jirgin Faransa zuwa Paris don duba lafiyarsa. Har yanzu ba a gano cutar dake damunsa ba tukun amma likitansa, Dr. Ashraf Kurdi yace ana bukatar gwaje-gwaje domin gano abinda yake damunsa amma yace babu alamar sankarar jini wadda ke jawo karancin jini. Dr. Kurdi yace Arafat na cikin hali mai kyau kuma yana cike da kuzari.

A cikin mako biyu da suka wuce ne Malam Arafat ya yi fama da abinda shugabannin Palasdinawa suka ce mura mai zafi wadda suka ce ta kazanta a ranar laraba wanda ya yi sanadiyar sumansa. Amma yanayinsa yanzu ya inganta. Hotunan da mataimakansa suka bayar sun nuna shi cike da kasala.

Malam Arafat bai bar gidansa ba tun shekara ta dubu biyu da daya saboda gudun kada Isra’ila ta kama shi ko kuma ta hana shi dawowa. Amma sakamakon rashin lafiyarsa Isra’ila ta amince da ya bar gidansa ta kuma ce za ta kyale shi ya dawo.

XS
SM
MD
LG