Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush da Abokin hamayar sa John kerry suna kampe na karshe. - 2004-11-01


Shugaba Bush da abokin hamarya sa John kerry suna cigaba da matsa kaimi a wani yunkuri na karshe domin samun kuri'u daga jama'a, kwana biyu kamin Amurkawa su zabi sabon shugaban su. Mr Bush ya halarci jimilar gangami hudu a jiya lahadi a biranen Florida da Ohio, yayinda shi kuma Sanata Kerry ya yi ibada a wani Choci a Ohio kamin ya zarce zuwa wajen gangamin kampe a Florida da new Hampshire.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan nan ta nuna cewa, 'yan takarar biyu sunyi kunnen doki a duk fadin kasar inda kowa a cikin su ya samu kashi 48% bisa 100. Bayanen ra'ayin jama'ar da aka samu daga jiha zuwa jiha sun nuna, kowane daya daga cikin su ya na iya samun kuri'u 270 da ake bukata domin zama shugaban kasa.

A ranar asabar, 'yan takarar jam'iyun biyu sun soki juna sosai bayan da aka fitar da sabon video na jawabin Osama bin Laden. Shugaba Bush a lokacin, ya kira abokin hamayar sa raggo, yayainda shi kuma Kerry ya ce in ya zama shugaban kasa zai fi iya aiwatar da yakin da ta'addanci mai inganci da ma'ana, wanda zai yi tasiri.

XS
SM
MD
LG