Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam ya kashe mutum uku ya raunata talatin da biyu a Kasuwar Tel-Aviv - 2004-11-01


Wani Bapalasdine dan kunan bakin wake ya tarwatsa bom din da ya yake dauke da shi a wata kasuwa dake cike da mutane a Tel –Aviv ranar litinin wanda ya kasha mutum uku. Mutane talatin da biyu kuma sun sami raunuka.

Tashin bom din ya fasa wani kanti da ake sayar da madara da dangoginta a wani sashe na kasuwar.Ma’aikatan ceto sun isa wurin inda suka tarar da matattun da kuma wadanda suka samu raunuka a cikin tarkacen fasassun rumfunan. Kungiyar neman ‘yancin ‘yan Palsdinu ta Popular Front for the Liberation of Palestine ta dauki nauyin kai wannan hari na kunar bakin wake kuma ta ce dan kunar bakin waken ya zo ne daga sansanin ‘yan gudun hijira na Askar da ke yamma da bakin kogi na garin Nablus.

Minista a hukumar mulkin Palasdinawa Saeb Erekat ya yi Allah wadai da harin sannan ya nemi kasashen duniya da su dawo da tattaunawa kan samar da zaman lafiya . Ya ce wannan ita ce hanyar da za a kawo karshen yawan tashe-tashen hankula.

Harin ya zo a lokacin da ake samun damuwa kan samun tashin hankula a tsakanin bangarorin ‘yan Palasdinu a kokarin cike gurbin da Yasser Arafat ya bari bayan da ya tafi neman magani a Faransa kwanaki uku da suka wuce.Isra’ila ta ce za ta kara yin hakuri a yakinta da ‘yan tada zaune tsaye a lokacin da Arafat bayanan don gudun kada ta kara dagula lamarin.

Harin kunar bakin wake na karshe an kai shi ne a ranar ashirin da biyu ga watan Satumba a inda wata Bapalasdiniya ta fasa bam da ke jikinta a kusa da wani wajen shiga motoci a Jerusalem wanda ya kashe ‘yansandan Isra’ila guda biyu. A ranar talatin da daya ga watan Agusta ‘yan kunar bakin wake na kungiyar Hamas sun kai hari kan motocin bas guda biyu masu zirga –zirga a tsakiyar birnin Isra’ila yankin Beer Sheva wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum goma sha shida. A watan da ya wuce sama da mutum talatin suka mutu sakamakon wasu hare-hare na daban-daban a wurin shakatawa na ‘yankin kogin Red Sea na Misra.

Hare-haren na otal din Hilton a Taba da wasu wurare biyu an kaisu ne kan ‘yan Isra’ila.

XS
SM
MD
LG