Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa suna zaben shugaba cikin rashin sanin mai yin nasara - 2004-11-02


Bayan dogon jira yanzu zaben da ake sauraro a Amurka ya zo. A yanzu Amurkawa na zaben shugaban da su ke so ya mulke su a zaben da dukkanin ‘yan takarar biyu shugaba Bush da senata Kerry su ke kan –kan .Sun sha yawon kamfe na karshe. Ga shugaba Bush, ranar karshen ta fara a can saman tsakiyar yamma da ke can jihar Ohio a inda ya ce, ‘’babu gaggawa a yin taron kamfe da duku-duku a wannan birni mai mahimmanci.’’

Shi kuwa John Kerry ya ziyarci Florida ne a inda ya ce ,‘’kuna son ku yi nasara, ku gama da wannan batu kuma ya zama an gama aikin gaba daya ?’’ Muryarsu ta nuna gajiyawa amma da alamar kuzari tare da su lokacin da ‘yan takarar suka shiga kamfen na karshe.Shugaba Bush ya danganta zaben da zuwa karshen doguwar tsere.’Ga layin karshen nan na hango shi, da alama kuma ina cike da karfi da kuzarin kaiwa ga gaci.’’A kamfen din karshe an bada karfi kan jawo hankalin magoya baya na kusa da kuma wadanda ba su yanke shawara kan wanda za su zaba ba.

A ranar litinin shugaba Bush ya bayyana manufofinsa a jihohi shida a inda ya fara da Ohio ya kuma kare a jiharsa ta Texas. A ko ina sakon daya ne, ‘’ Tabbatar da cewa abokanka da makwabtanka sun jefa kuri’unsu, ‘yan republicans su fito ‘yan indipenda masu wayo da ‘yan Democrat masu lura duka.’’

Fitowar masu zabe na da mahimmanci amma a zaben da ake kan –kan yana da matukar mahimmanci.Saboda haka a lokacin da ‘yan takarar su ke ta yin jawabai masu goyon bayansu suna ta famar aika sakwanni ta hanyar wayar sadarwa da kuma bi gida –gida don jan hankalin masu jefa kuri’a.. A wani taro a Wisconsin cikin jihohin da ya ziyarta ranar litinin senata Kerry ya ce kokarin masu jefa kuri’a zai tabbatar da samar da banbanci. ‘’Ina bukatar ku don in gudanar da aiki tukuru. Ku bi gida-gida, ku aika sakwanni ta waya , ku yi magana da abokanku don a tabbatar da sauya alkiblar wannan kasa tamu’’

A lokacin kamfen din, yaki da ta’addanci da harkar Iraqi da abubuwan da suka shafi tattalin arziki sune suka yi katutu. Shi shugaba Bush ya ce senata Kerry ba shi da karfi halin da ya dace ya shugabanci Amurka a inda shi kuma senata Kerry ya ce duniya gaba daya suna sa ido domin ganin yadda Amurkawa za su yi a ranar zabe saboda haka ranar yanke hukunci ne a Amurka

XS
SM
MD
LG