Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush da John Kerry, abokin hamayar sa sun cigaba da yakin neman zabe ba ji-ba-gani. - 2004-11-02


Shugaba Bush ya kammala yakin neman zaben sa tare da halartar tarurukan kampe har guda bakwai, da fatan samu galaba a zaben da ake ganin yana kud-da kud kwana daya kuma kamin jama'a su soma kada kuri'a.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da gidan talabijin na CNN ya gudanar, a yanzu ya ba John Kerry na jam'iyar Damokarat dan rinjaye na kashi hudu a jihar Ohio. Shi kuwa shugaba Bush ya yi kokarin shan gaban abokin takarar sa ta yin gangamin yakin neman zabe a daren lahadi a biranen Cincinnati da Wilmington a jiya da safe.

Shugaba Bush ya ce " Ban ga inda ya kamata in karasa yakin neman zabe na ba in ba da mutanen jihar Ohio ba." Ya cigaba da cewa "Ina son in yi muku godiya, in gode muku akan goyon bayan ku, da kuma taimakon ku zamu lashe wannan muhimmiyar jihar muku ma ci zaben gobe." Yace na zo nan ne domin in nemi taimakon ku. Ku yi kokari ku sa abokan ku da makwabtan ku su fita su kada kuri'ar su.Shugaba Bush ya sheda ma duban jama'ar cewa Amurka tana bukatar tsayayen shugaba mai kwarjini da karfin hali kuma shi a shirye yake yayi wannan jan aikin shugabanci Amurkar.

Mr Bush yace tilas ne shugaban amurka yayi shugabanci gaba-gadi batare da wani boye-boye ba. Yace duk shugabannin da suka gabata, kama daga Lincoln zuwa Reagan sun nuna a fili cewa shugaba baya jin tsoro balantana ma ya rinka sauya matsayin sa kamar yadda iska ke kadawa. Shugaba inji Mr Bush, ya kan dauki tsauraran matakai ko yanke shawara mai zafi ya kuma kare matsayin sa. Shugaban yayi gangamin neman kuri'a daga magoya bayan sa a pennsylvania,a can waje da yammacin birnin Pittsburgh. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna Mr Bush na kan gaba da Sanata Kerry da maki hudu a Pennsylvania yayinda a Wisconsin yana gaba da maki hudu bayan yakin neman zabe a birnin Milwaukee.

XS
SM
MD
LG