Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush na cike da yakinin samun nasarar zabe - 2004-11-02


Shugaba Bush da uwargidansa Laura da ‘yayansa tagwaye mata sun jefa kuri’unsu a rumfar zabe ta tamanin a wani ofishin ma’aikatan kashe gobara da ke Crawford, Texas kusa da gidan gonarsu. Wasu magoya baya da su ke wurin sun yiwa Bush da iyalinsa kirari da shewa a bayan ‘yansanda da ke kewaye da su.

Rike da hannun uwargidansa shugaba Bush ya gayawa ‘yan jarida cewa yana cike da yakinin samun nasarar kara shekara hudu a ofis. ‘Wannan zabe yana hannun jama’a kuma ina cike da kwanciyar hankali game da wannan.Mutane sun san kan abinda na tsaya. Na ji dadin wannan kamfen . Ya kasance wani darasi ne mai dadi na tafiye –tafiye cikin kasa ina magana kan abinda na yi imani da shi kan kuma yadda zan jagoranci wannan kasa na karin shekaru hudu.Abin sha’awa ne cewa mutane za su yanke matakin da ya dace kuma na yi imani zan samu nasara.’’

A abinda shugaban yace ranar kamfen dinsa ce ta karshe shugaban bai bar komai ba a inda ya yi awowi goma sha tara da tsayawa bakwai a jihohi shida .Mista Bush ya gayawa ‘yan jaridu cewa ya kammala kamfen kuma yana cike da nutsuwa da kuma kwarin gwiwa kan hukuncin mutane. ‘’ Akwai abubuwa da dama da muka yi mahawara akansu babban batu na yaki sai zaman lafiya da tattalin arziki. Ina da manufa wanda kowa ya fahimta. Ina da cikakkiyar fahimtar yadda ya kamata in yi jagoranci amma za mu ga yadda abu zai kasance yau da daddare. Kune masu yin hasashe to za mu ga abinda mutane suke so. Yanzu lokacin da mutane za su yanke shawara kan abinda suke so ne.’’

Shugaban ya ce wannan zabe ne na wanda mutane suke so su amincewa ya mulke su ya kuma ce ya gamsu cewa ya nuna banbanci tsakaninsa da senata Kerry na Democrat. ‘’Wa kuke tsammani zai iya tsare kasa? Wa kuke tsammani zai zama tsayayye kuma kaifi daya wajen kare Amurka? Wa zai zama mai bin ka’idojin da yawancin mutane suka yarda da su kuma ya sanya a samu karuwar tattalin arziki?’’ Bayan tsayawa a Ohio domin godewa magoya baya masu aikin zabe Bush da iyalansa sun dawo fadar gwamnati ta White House domin sauraron sakamakon zaben.

XS
SM
MD
LG