Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben shugaba kasa yana tafiya kafada-da kafada - 2004-11-03


Har yanzu kuma, zaben shugaban kasa a Amurka yana nan gab-da-gab bayan ma an rufe jefa kuri'a kuma ba san ko kwana nawa za'ayi kamin a samu sakamakon zaben ko sa'oi nawa za'ayi. Wannan karon an mayar da hankali ne akan jihar Ohio inda aka fi fafatawa.

Lamarin ya zama tamkar jiki ga masu zabe a Amurka. An soma zaben na shekara ta 2004 daga safe har zuwa can wani lokaci da tsakiyar dare batare da samun wanda yayi nasara kai tsaye ba. A zaben shekara ta 2000 jihar Florida ce ta tantance yadda zaben ya kaya, a yanzu kuma dai da alama jihar Ohio ce zata yanke hujja akan sakamakon zaben. Bayan dai an kirga sama da kashi tis'in na kuri'ar da aka jefa a jihar Ohio, Shugaba Bush na kan gaba kuma mai yuwa jihar ta samar da adadin kuri'ar da yake nema ya lashe zaben.

Amma, jami'an yakin neman zaben John Kerry sun ki su amince ba su ci zabe a jihar Ohio ba. sun nace sai an kirga dubun-dubatar kuri'u da ba'a kirga ba tun daga farko wadanda suka hada da na wucen gadi na jama'ar da ke jiran a tantance sunayen su a kundin tsara sunayen masu zaben. Bayan an bude runfunan jefa kuri'a, Kungiyoyin yakin neman zaben 'yan takarar biyu sun bayana fatar, za'a samu sakamakon zaben batare da wani jinkiri ba kamar yadda aka samu rudani a zaben shekara ta 2000. Shugaba Bush ya sheda ma 'yan jarida bayan ya kada kuri'ar sa a kusa da gidan gonar sa, cewa yana fatan ba za'a samu jinkiri ba a sakamakon.

XS
SM
MD
LG