Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Isra’ila da na Palasdinawa  suna taro kan halin da Arafat ke ciki - 2004-11-04


Shugabannin Isra’ila da na Palasdinawa sun yi taro a yau don fara tsara makomar gaba wadda za ta kasance ba tare da Yasser Arafat ba a lokacin da aka samu labarin cewa Arafat dan shekara saba’in da biyar ya yi doguwar suma a wani asibitin soja dake Faransa. Shugabannin Palasdinawa sun tabbatar da tsanantar halin da Yasser Arafat ke ciki wanda ya sanya suka garzaya garin Ramallah da ke ‘yankin yammacin kogi don yin taron gaggawa.Tsohon firaministan Palasdinu Mahmoud Abbas ya shirya tashi zuwa Paris a safiyar Alhamis amma ya jingine tafiyar da aka shaida masa cewa ba zai samu damar ganin Malam Arafat ba. Dan uwansa Nasser al-kidwa da wakilin kungiyar PLO a Faransa,kawai ake kyalewa suke ganinsa akai-akai. Jami’an tsaron Isra'ila sun mayar da hankalinsu ne kan yanayin da shugaban Palasdinawa ke ciki a taronsu na mako-mako. Isra’ila na kokarin yin wani shirin gaggawa kan koda Arafat ya rasu su san yadda za su yi da wani kokari da zai iya faruwa na binne shi a Jerusalem. Firaminista Ariel Sharon ya ce ba zai taba kyale hakan ta faru ba. Shi dai shugaban Palasdinawan da dadewa ya taba bayyana burinsa na a binne shi a wurin da musulmi ke kira Haram a-Sharif ko kuma wuri mai daraja wanda kuma yahudawa ke kira tudun ibada. Jami’an tsaron Isra’ila suna damuwa kan cewa jerin gwanon binne shi ta tsakiyar Jerusalem zai tara mutane masu yawan gaske wanda ke iya jawo wahalar lura da su ko kuma a kasa rula da su gaba daya. Idan kuma ta kasance Arafat ya rasu Isra’ila na shirin gaggawa kan yadda za ta shawo kan fitinu da ka iya tasowa a sakamakon rigingimu tsakanin kungiyoyin Palasdinu daban-daban kan wanene zai gaje shi.

XS
SM
MD
LG