Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Amurka da na Iraqi sun doshi Fallujah - 2004-11-08


Dakarun Amurkan da na Iraqi sun matsa daga yammacin garin inda ‘yan gwagwarmayar Iraqi suka ja daga a Fallujah kuma tuni suna rike da babban asibitin birnin da kuma mahimman gadoji guda biyu wanda suke kan kogin Euphrates.Wadannan gadoji sune hanyoyin fita daga Fallujah ta yamma.An kuma samu labarin kaurewar fada a wajen birnin a lokacin da jiragen saman yakin Amurka da kuma bindigogin igwa suka ci gaba da kai hari kan sansanonin ‘yan gwagwarmayar. An samu kuma labarin cewa dakarun kawance suna shan farmaki na manya da kananan bindigogi.

An fara kai hararen farko kan Fallujah ne bayan da firaministan rikon kwarya Iyad Allawi a ranar lahadi ya bayyana dokar ta baci na kwana siitin a bangarorin kasar da dama.Dubannin dakarun Amurka da na Iraqi sun taru a bakin garin Fallujah suna jiran umarnin kai farmaki kan birnin.

A ranar lahadi ‘yan gwagwarmaya sun kashe akalla ‘yan sandan Iraqi ashirin da daya a yammacin garuruwan Haditha da Haqlaniya

XS
SM
MD
LG