Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Palasdinawa za su ziyarci Arafat a Paris - 2004-11-08


Shugabannin Palasdinawa na ci gaba da shirinsu na zuwa Paris domin ganawa da likitocin Faransa kan rashin lafiyar Yasser Arafat duk da rashin yardar uwargidan Arafat din. Firaminista Ahmed Qureia da tsohon firaministan Mahmoud Abbas da ministan harkokin kasashen waje Nabil Sha’ath yanzu ana sa ran za su tashi zuwa Paris don tattaunawa da likitocin Arafat a ranar talata.

Tafiyar, da an shirya yinta ne ranar litinin amma aka daga saboda zargin da uwargidan Arafat ta yi a gidan talabijin na al-Jazeera cewa shugabannin Palasdinawa na yiwa Arafat din makirci.Suha Arafat ta ce wasu daga cikin shugabannin Palasdinawan wadanda ke son maye kujerarsa na kokarin binne shi da rai a inda ta ce mijinta na cikin koshin lafiya kuma zai koma gida.

Yasser Arafat ya kasance yana jinya a asibitin soja a wajen Paris tun sama da mako daya da ya wuce. Babu bayani kan irin cutar dake damunsa amma akwai jita-jita mai yawa kan irin halin da yake ciki. Likitocin Faransar sukan ce yana cikin hali mai ban tsoro amma kuma babu wani hatsari.Wasu shugabannin Palasdinawa sun ce ya yi doguwar suma wasu kuma sun ce ba haka abin yake ba. Akwai gwagwarmaya kan maye matsayinsa idan ta kasance Arafat din ya rasu.

Bangarorin shugabannin Palasdinawa sun yi tarurruka a yammacin bakin kogi da kuma Gaza domin samun hadin kai da kuma gudun samun rikice-rikice a wajen samun wanda zai maye Arafat idan ya rasu. Su ma jami’an Isra’ila sun yi shirin fuskantar duk wani rikici da ka iya tasowa idan Arafat ya rasu.

Akwai kuma maganar inda za’a binne shugaban Palasdinawan idan ya rasu. An ce shi dai ya ce ya fi so a binne shi a tsohon birnin Jerusalem abinda gwamnatin Isra’ila ta ce ba zai yiwu ba. Gaza shine wurin da ake tunanin za’a binne shi amma babu tabbas. Jana'izar ta iya kasancewa a ko ina ,da alama Alkahira inda shugabannin kasashe musamman kasashen larabawa za su iya halarta.

XS
SM
MD
LG