Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Amurka da na Iraqi na rike da kashi saba’in na - 2004-11-10


Dakarun Amurka da na Iraqi sun kara dannawa zuwa cikin Fallujah ta cikin lunguna a kokarinsu na sake kwato birnin daga hannun ‘yan gwagwarmaya. Rahotanni sun ruwaito jami’an sojin Amurka suna cewa a yanzu dakarun kawance suna rike da kashi saba’in na birnin. Amma sun ce akwai ‘yar tarjiya har yanzu daga wajen ‘yan gwagwarmayar.

Babban kwamandan dakarun Amurka, Laftana-janar Thomas Metz a ranar talata ya ce dakarun kawancen sun karya lagwan ‘yan gwagwarmayar a hare-haren kwana biyun farko amma ya ce har yanzu akwai sauran fafatawa. Ya kuma ce mutumin da aka fi nema a Iraqi, dan ta’adda Abu Musa al-Zarqawi da alama ya fice daga birnin tun kafin fara kai harin.

Rundunar sojin Amurka ta ce an kashe sojojinta goma na Iraqi guda biyu tun fara kai wannan harin a ranar litinin. Ta kuma ce an kashe ‘yan gwagwarmayar da dama fiye da yadda akai tsammani amma ba ta bayar da adadi ba. Da yawa daga cikin mazauna Fallujah sun bar birnin kafin fara kai harin.

XS
SM
MD
LG