Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush ya gayyaci shugabannin Musulmi shan ruwa - 2004-11-11


Shugaba Bush ya gayyaci shugabannin Musulmi shan ruwa a fadar gwamnati ta White House a cikin wannan watan azumi na Ramadan. Bush ya ce kasar Amurka tana da karfi kuma cike da buri saboda irin kyauta da tausayi na Musulmin Amurka kuma saboda irin kyakkawar dangantaka da ke tsakaninta da abokanta Musulmi a fadin duniya. ‘’Ga Musulmi a Amurka da sauran duniya, watan Ramadan wani lokaci ne na musamman na yin nazari da azumi da kuma sadaka’’ in ji Mista Bush. ‘’Lokaci ne na tunawa da masu karamin karfi da kuma bayar da kyaututtuka ga wanda ba su da shi.

Lokaci ne na ibada da adduoi. Kuma irin adduoin da Amurkawa Musulmim ke yi ga Amurka abu ne mai alheri ga kasa. A wannan lokaci na zaman tar eda kuma godiya ga Allah Bush ya ce Musulmi a Amurka na tuna ‘yan uwansu da suke nesa wanda rayuwarsu a yanzu na samun ‘yanci da kuma fata.

‘’A Iraqi iyalai suna azumi cikin ‘yanci bayan da suka yi fama da danniya da fargaba. Mutanen Iraqi suna jan akalar kasarsu zuwa ga dimukuradiyya a inda za su zabi shugabanninsu a watan Janairu,’’ in ji Bush. Shugaban ya ce zaben da aka shirya yi Iraqi da kuma wanda aka yi a Afghanistan wasu abubuwa ne na alfahari ga Amurka a kokarinta na tabbatar da fata ga kasashe.’Yanci ba kyautar Amurka ce ba ga duniya amma kyauta ce daga Allah ga kowa da kowa’.

A lokacin da shugaba Bush yake kare samar da ‘yanci da adalci a kasashen duniya ya ce dole ne Amurkawa su tabbatar da wadannan dabi’u a cikin gida.’’ A lokacin kafa wannan kasa mun yi alkawarin tabbatar da adalci da hakuri da juna mun cika wannan alkawarin. Ba ma kabilanci ko nuna bambancin addini ta kowacce hanya. Muna girmama kowa da kowa da addininsa kuma muna kare ‘yancin yin bauta ga Allah ba tare da wani tsoro ba,' in ji Bush

Wannan shan ruwa na shugaba Bush a fadar gwamnati ta White House ya biyo bayan irinsa sama da sittin da aka shirya a ofisoshin jakadancin Amurka a kasashen duniya. Jakadun Amurka sun shirya shan ruwan ne domin kara samar da fahimta tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba.

XS
SM
MD
LG