Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush ya yiwa Palasdinawa ta ‘aziyyar Arafat - 2004-11-11


Shugaba Bush na Amurka ya yiwa Palasdinawa ta’aziyyar mutuwar shugabansu Yasser Arafat. Bush ya ce mutuwar Arafat wani mahimmin lokaci ne a tarihin Palasdinawa ya kuma yi fatan cewa nan gaba za a samu cimma burin kafa ‘yantacciyar kasa mai bin tafarkin dimukuradiyya wadda ke zaman lafiya da makwabtanta.

A wani sako da aka rubuta, shugaba Bush ya ce a wannan lokaci ya zama dole kasashe su hada karfi don cimma burin samar da zaman lafiya. A lokacin da yake magana kafin rasuwar Arafat bayan taro da babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO shugaba Bush ya ce za a iya samun zaman lafiya a gabas ta tsakiya muddin Palasdinawa suka zabi shugaban da zai yi watsi da tada hankali.’’Akwai hanyar samar da zaman lafiya idan shugabannin Palasdinawa suka nemi a taimaka musu don ci gaba ta hanyar samar da kasa mai bin tafarkin dimukuradiyya da kuma ‘yanci.

Idan aka samu haka na yi imani za’a kuma a samu domin mutane suna son zama cikin ‘yanci, Amurka za ta yi kokarin taimakawa wajen kafa cibiyoyin da ake bukata domin samun al’umma mai ‘yanci wanda kuma zai sanya Palasdinawa su samu kasarsu.

Tare da hadin kan tarayyar turai ta EU da majalisar dinkin duniya da kuma kasar Rasha Mista Bush ya samar da wani shiri mai suna taswirar zaman lafiya a gabas ta tsakiya wanda ya hada da yarjejeniyoyi da shirye-shiryen tsaro domin tabbatar da samar da kasar Palasdinu mai ‘yanci tare da ta Isra’la. Amma shirin ya hadu da tashe-tashen hankula a yankin. Kokarin dawo da wannan shirin samar da zaman lafiya na cikin abinda za a tattauna a lokacin taro tsakanin Mista Bush da Firaministan Birtaniya Tony Blair.

XS
SM
MD
LG